logo

HAUSA

Lokacin Guyu lokaci ne da furannin peony kan fito

2022-04-20 15:07:22 CMG Hausa

Yau 20 ga wata, rana ce ta Guyu ko kuma Grain Rain a Turance, wato bisa tsarin alamu 24 na sauyawar yanayi cikin shekara da kaka da kakanin Sinawa suka kirkiro.Lokacin Guyu, lokaci ne da furannin peony kan fito, don haka Sinawa kan kira nau’in furen da suna“furen Guyu”. A lokacin Guyu, a kan kuma gudanar da bukukuwan nune-nunen furannin peony a wasu sassan kasar Sin.(Lubabatu)