logo

HAUSA

Shugaban kasar Kwadebuwa ya nada mataimakinsa da firaminista

2022-04-20 10:17:03 CMG HAUSA

 

A jiya Talata, shugaban kasar Kwadebuwa, Alassane Ouattara, ya nada Tiemoko Meyliet Kone, gwamnan babban bankin kasashen yammacin Afrika (BCEAO), a matsayin mataimakinsa.

Shugaba Ouattara, ya sanar da nadin ne a lokacin jawabin da ya gabatarwa ’yan kasar a ranar Talata a Yamoussoukro, babban birnin kasar mai tazarar kilomita 230 daga Abidjan, birnin kasuwancin kasar.

An haifi Tiemoko Meyliet Kone a shekarar 1949, an nada shi a mukamin gwamnan BCEAO a ranar 17 ga watan Augustan shekarar 2020, inda aka zabe shi a wa’adi na biyu na shekaru shida na gwamnan bankin, a lokacin babban taron shugabannin kasashe da na hukumomin kudi na yammacin Afrika (UMOA).

Bugu da kari, Ouattara ya kuma nada Patrick Achi, a matsayin firaministan kasar, wanda ya yi murabus daga kan wannan mukami na firaminista a gwamnatin kasar a makon da ya gabata.

Patrick Achi, ya gabatar da takardarsa ta yin murabus a ranar 13 ga watan Afrilu a Abidjan, da na mukarraban gwamnati kasar, biyo bayan bukatar da Alassane Ouattara ya nema, domin ya samu damar sake kafa gwamnati. Shugaba Ouattara, ya amince da takardar murabus din da ya gabatar, sannan ya yi alkawarin nada sabon firaministan kasar, wanda zai jagoranci aikin tantancewa da kuma zabar majalisar ministocin kasar 30, maimakon 45 da ake da su, bisa lura da yanayin koma bayan tattalin arziki da duniya ke fuskanta a halin yanzu. (Ahmad Fagam)