logo

HAUSA

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya amsa tambaya game da rasuwar jakadan kasar Philippine a kasar Sin

2022-04-19 17:22:22 CMG Hausa

Tambaya: An ce jakadan kasar Philippine a kasar Sin Jose Santiago L. Sta. Romana ya rasu a kasar Sin a ranar 18 ga watan nan da muke ciki. Ko gwamnatin kasar Sin na da karin bayani dangane da batun?


Amsa: Bangaren kasar Sin ta kadu sosai game da rasuwar jakada Romana. Mista Romana ya shahara sosai a fannin fahimtar al'adun kasar Sin, kana ya dade yana aiki a kasar Sin, wanda ya kasance aminin Sinawa. Bayan da ya zama jakadan kasar Philippine a Sin, ya yi kokarin aiki don kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2, da karfafa zumunta tsakanin al'ummun kasashen, inda ya samar da gudunmowa sosai. Bangaren Sin yana matukar bakin ciki game da rasuwarsa, ana kuma jajantawa iyalansa. Za a yi hadin gwiwa da iyalan jakada Romana da gidan jakadancin Philippine dake kasar Sin, don daidaita al'amura masu biyo baya, gami da kokarin samar da sauki ga dukkan ayykan da za a gudanar. (Bello Wang)