logo

HAUSA

An kaddamar da Lambun Tsirrai Na Kasar Sin a birnin Beijing

2022-04-19 11:18:28 CMG HAUSA

 

            

Jiya ne, hukumar kula da gandun daji da ciyawa ta kasar Sin, ta sanar da kaddamar da “Lambun Tsirrai Na Kasa” a birnin Beijing a hukumance.

Lambun da aka tsara mai fadin yanki da ya kai kadada 600, an gina shi ne bisa aikin cibiyar nazarin halittu wadda ke karkashin kwalejin kimiyyar kasar Sin da lambun tsirrai na birnin Beijing.

Lambun yana da nau’o’in tsirrai sama da 30,000 da samfuran tsirrai miliyan 5 daga nahiyoyi biyar na duniya.

A cewar hukumar, Lambun wani tushe ne na kare ire-iren shuka na kasa, kuma muhimmiyar alama ce ta matakin ci gaba mai dorewa a kasar.

A kokarin da take yi na karfafa kariyar halittu, kasar Sin na hanzarta gina tsarin lambunan tsirrai na kasa a wurare kamar Beijing da Guangzhou.

A watan Disamban shekarar 2021 ne, majalisar gudanarwar kasar, ko majalisar ministoci, ta amince da kafa lambun tsirrai na kasa a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. (Ibrahim)