logo

HAUSA

Kasar Sin za ta bunkasa tallafin kudi don inganta tattalin arzikin kasa na hakika

2022-04-19 14:06:44 CMG HAUSA

 

Hukumomin kudi na kasar Sin, sun bayyana a jiya Litinin cewa, kasar ta kaddamar da wasu matakai na karfafa tallafin kudi ga tsarin tattalin arzikin kasar.

Wata sanarwa da babban bankin kasar Sin da hukumar kula da harkokin wajen kasar suka fitar cikin hadin gwiwa ta bayyana cewa, kasar za ta kara tallafin kudin da take bayarwa, don rage wahalhalun da kasuwanni ke fuskanta, da tabbatar da gudanar tattalin arzikin kasar ba tare da wata tangarda ba, da inganta fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje.

Sanarwar ta ce, kasar Sin za ta kara tallafin kudade ga masana'antu, da kamfanoni da mutanen da annobar COVID-19 ta shafa, da jagorantar cibiyoyin hada-hadar kudi, don kara yawan basussukan da ake bayarwa, da yin rangwamen da ya dace ga tsarin tattalin arziki, da samar da kudade na bai daya ga kananan masana’antu da kananan kamfanoni.

Bugu da kari, sanarwar ta bayyana cewa, ya kamata cibiyoyin hada-hadar kudi, su magance bukatun kudade a bangaren sufuri da masu samar da hidima da direbobin manyan motoci, kana su tsara shirye-shirye masu ma'ana, don tsawaita wa’adin biyan basussuka ko sabuntawa kamar yadda ya dace, idan har wadannan bangarori na fuskantar matsaloli wajen biyan basussukan da suka karba sakamakon annobar COVID-19.   (Ibrahim)