logo

HAUSA

Muhallin Halittu Ya Kyautatu Sosai A Kasar Sin A Shekarar 2021

2022-04-19 10:58:31 CMG Hausa

Jiya ne, aka gabatar da rahoton majalisar gudanarwar kasar Sin kan yadda aka cimma manufofin kiyaye muhalli a shekarar 2021, ga taro na 34 na kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 13 don ya yi nazari a kai.

Ministan kula da kiyaye muhallin halittu na kasar Sin, Huang Runqiu ya bayyana cewa, a shekarar 2021, muhallin halittu a kasar Sin ya kyautatu sosai. Kasar Sin ta cimma manufofin kiyaye muhallin halittu a fannoni guda 8 yadda ka kamata kamar yadda shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar ya tsara. Inda ya ce, Ingancin iska ya ci gaba da samun kyautatuwa a duk fadin kasar. Yawan kwanakin da aka samu iska mai kyau ya kai 87.5% bisa jimilar kwanakin shekarar 2021 baki daya, adadin da ya karu da 0.5% bisa makamancin lokaci na shekarar 2020. Haka kuma a shekaru 2 a jere ne, yawan adadin sinadaran dake gurbata iska na PM2.5 da laimar Ozone (O₃) dukkansu sun ragu. Yawan biranen da suka yi nasarar aiwatar da manufar kyautata iska ya kai 218 a duk kasar, adadin da ya karu zuwa guda 12 bisa makamancin lokaci na shekarar 2020. Har ila yau yanayin ruwan da ke doron kasa ya ci gaba da samun kyautatuwa a kasar ta Sin. Ruwan da ke cikin kogin Yangtze, da kogin Zhujiang, duk suna da inganci sosai, yayin da ruwan da ke cikin rawayen kogi ya samu kyautatuwa.”

Dangane da shirin ayyukan kiyaye muhallin halittu a shekarar 2022 da muke ciki kuma, rahoton ya yi nuni da cewa, wajibi ne a kara mai da hankali kan yaki da gurbata muhalli bisa halin da ake ciki kuma ta hanyar kimiyya bisa dokoki, haka kuma, ya kamata a yi kokarin rage gurbata muhalli da rage fitar da iskar carbon dioxide mai dumama yanayin duniyarmu tare, da gudanar da ayyukan yaki da gurbata muhalli, da kiyaye muhalli, da tinkarar sauyin yanayi yadda ya kamata, a kokarin kara zama kan sauya hanyar raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasa zuwa hanya maras gurbata muhalli daga dukkan fannoni. (Tasallah Yuan)