logo

HAUSA

Farfagandar kyamar kasar Sin ba za ta yi kasuwa a tsibiran yankin Pacific ba

2022-04-19 21:33:08 CMG Hausa

A kwanan nan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ya bayyana cewa, fadar White House ta Amurka ta shirya tura tawagar musamman karkashin jagorancin Mr. Kurt Campbell, jagoran tsare tsare na ayyukan da suka shafi yankunan tekun Indiya da Pacific a majalissar tsaron kasa, zuwa tsibiran dake yankin, ciki har da tsibirin Solomon.

Kakakin ya ce tawagar Amurka na sa ran tattauna batutuwa da dama, ciki har da wadanda suka jibanci kasar Sin yayin wannan ziyara.

A baya bayan nan, Sin da tsibirin Solomon sun sanya hannu, kan yarjejeniyar cudanya a hukumance, don gane da hadin gwiwar tsaro, sun kuma amince su hada hannu wajen tabbatar da doka da oda, da kare rayukan al’umma da duniyoyin su, da ba da agajin jin kai, da aiwatar da matakan ceto yayin aukuwar bala’u, da sauran fannoni, karkashin tsari na daidaito da cimma moriyar juna. Wannan hadin gwiwa ya yi daidai da dokokin kasa da kasa, da kuma tsarin cudanyar sassa, kuma ba a yi shi domin nuna yatsa ga wata kasa ko yanki ba.

Ko shakka babu, kasashen yankin Pacific, ba ‘yan koren wani bangare ba ne, balle a yi amfani da su wajen rarraba kan wasu sassa, ko fito na fito da wani bangare. Maimakon haka, tsibirai ne dake da fatan fadada hadin gwiwa da kasashen waje, suna kuma da ikon zabar abokan hulda bisa radin kan su.  (Saminu)