logo

HAUSA

Rikicin Rasha da Ukraine ya shafi kasashen Afirka dake shigo da mai da alkama

2022-04-19 11:18:57 CMG HAUSA

              

Shugaban asusun Fairfax Africa, wani kamfanin zuba jari na kasa da kasa mai hedkwata a birnin Washington na kasar Amurka, Zemedeneh Negatu, ya bayyana cewa, duniya tana ganin irin tasirin da rikicin kasashen Rasha da Ukraine ya haifar. Amma rikicin ya fi yin mummunar illa ga kasashen Afirka dake shigo da alkama da mai.

Negatu ya bayyana yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya-bayan nan cewa, takunkuman da Amurka da kawayenta suka kakabawa kasar Rasha, sun kara ta’azza hauhawar farashin kayayyakin abinci a nahiyar Afirka, inda farashin man fetur da kayayyakin abinci yana karuwa cikin saurin.

A cikin rahotonsa na baya-bayan nan, babban taron MDD kan cinikayya da raya kasa ya bayyana cewa, kasashen Somaliya da Benin da Masar da Sudan da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Senegal da Tanzaniya, su ne kasashen Afirka da suka fi fama da rugujewar kasuwanni sakamakon takunkuman da kuma rikicin dake faruwa a kasar Ukraine.

A halin da ake ciki kuma, Negatu ya lura cewa, wasu kasashen Afirka dake fitar da mai, za su iya cin gajiyar hauhawar farashin danyen man. Sai dai kuma, irin wadannan kasashe dake fitar da mai kamar Najeriya, ba su tsira daga tasirin rikicin Ukraine da ke ci gaba da haifar da tsadar man fetur ba. (Ibrahim)