logo

HAUSA

Afirka ta Kudu ta ayyana dokar ta baci domin magance yawaitar ambaliyar ruwa

2022-04-19 16:06:42 CMG Hausa

Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya ayyana dokar ta baci a daren jiya Litinin, a yayin da aka yi kiyasin cewa, ambaliyar ruwar makon jiya, da ta yi mummunar illa a jihar KwaZulu-Natal, ta kai ta biliyoyin Rand na kudin kasar.

Shugaban ya ce, kwanan nan jihar KwaZulu-Natal ta fuskanci ambaliyar ruwa mafi muni da ba a taba ganin irinta ba tun shekarar 1987, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 440 tare da lalata gidaje, da harkokin kasuwanci, da tituna da gadoji. An kiyasta cewa, sama da mutane 40,000 ne ambaliyar ta raba da matsugunansu.(Ibrahim)