logo

HAUSA

Karin abokai sun shiga shawarar “ziri daya da hanya daya”

2022-04-19 14:07:47 CMG HAUSA

 

Yau Talata, hukumar zurfafa gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje ta kasar Sin, ta shirya wani taron manema labarai, inda kakakin hukumar Meng Wei ta yi bayani cewa, ya zuwa yanzu, Sin ta kulla yarjejeniyoyin hadin kai fiye da 200 karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”, tare da kasashe 149 da kungiyoyin kasa da kasa 32.

Rahotanni na cewa, daga farkon wannan shekara zuwa yanzu, kasar Sin ta kulla yarjejeniyoyi da kasashen Nicaragua da Syria da Argentina da Malawi da sauransu, karin abokai dake amincewa da shawarar.

A farkon rubu’in bana, jiragen kasa sun yi zirga-zirga tsakanin Sin da Turai sau 3630, kana yawan sundukan da aka yi jigilarsu, ya kai dubu 350, wadannan alkaluma biyu sun karu da kashi 7% da 9%, adadin jiragen kasa da aka yi amfani da shi a wata daya, ya kai fiye da dubu a cikin watanni 23 a jere da suka gabata. Matakin da ya ba da tabbaci ga tsare-tsaren samar da kayayyaki a duniya. (Amina Xu)