logo

HAUSA

Xi Jinping ya aike da sakon jaje ga shugaban Afirka ta kudu game da bala’in ambaliyar ruwa a KwaZulu-Natal

2022-04-19 17:04:11 CMG Hausa


Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike sakon jaje ga takwaransa na Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, don gane da bala’in ambaliyar ruwa da ta auku a yankin KwaZulu-Natal.

Cikin sakon na sa, Xi Jinping ya ce “Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka kwashe lokaci mai tsawo ana yi a KwaZulu-Natal na Afirka ta kudu ya haifar da ambaliya, da rasuwar mutane masu yawa, kana hakan ya haifar da asarar dukiyoyi da dama”. Ya ce “A madadin gwamnati da al’ummar kasar Sin, da ni kai na, ina amfani da wannan dama domin gabatar da sakon ta’aziyya da jaje ga iyalan wadanda wannan annoba ta shafa, da kuma fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.

Ya kuma yi imanin cewa, jagorancin Afirka ta kudu da kuma al’ummun kasar, musamman bangaren da wannan annoba ta shafa, za su shawo kan kalubalen da ake fuskanta, su kuma sake gina muhallan su cikin gaggauwa.  (Saminu)