logo

HAUSA

Zelensky: rundunar sojan Rasha ta kaddamar da hari kan Donbas

2022-04-19 11:03:29 CMG Hausa

Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar Ukraine ya bayyana a jiya Litinin cewa, sojojin kasar Rasha sun kaddama da hari kan yankin Donbas.

Kamfanin dillancin labaru na kasar Ukraine ya bayar da rahoton cewa, a cikin jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo a wannan rana da dare, Zelensky ya ce, rundunar sojan Rasha ta dade tana shirya kai hari yankin Donbas, inda ta tura sojoji masu yawa don kai harin a yankin na Donbas. Ya kara da cewa, duk yawan sojojin da Rasha ta tura zuwa yankin Donbas, kasar Ukraine za ta yake su, kuma ba za ta bar duk abin da ta mallaka ba.

Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Rasha Igor Konashenkov, ya bayyana cewa, jiya, mayakan saman Rasha sun harba makamai masu linzami kan wata cibiyar adana kayayyakin soja ta Ukraine dake yankin Lviv na yammacin Ukraine, inda aka latata makamamai masu tarin yawa da kasashen Amurka da Turai suka aika yau kwanaki 6 da suka wuce. (Tasallah Yuan)