logo

HAUSA

Wang Wenbin: Amurka na kara zama kasa da ake keta hakkin bil adama a cikin ta

2022-04-18 20:20:19 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin na matukar damuwa game da yanayin tabarbarewar hakkin bil adama a Amurka, inda shaidu da dama ke nuna yadda batun nuna wariyar launin fata, da laifuka masu alaka da harbin bindiga, da yadda jami’an tsaro ke amfani da karfi fiye da kima ke kara ta’azzara.

Wang, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na Litinin din nan, ya ce wadannan laifuka masu nasaba da keta hakkin bil adama sun jima suna gudana, sun kuma ratsa dukkanin sassan kasar.

Jami’in ya ce a bana ake cika shekaru 30, tun bayan da kasar Sin ta shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD a karon farko. Kuma a yanzu Sin ta zamo kasa ta 2, mafi ba da tallafi ga ayyukan na MDD, kana kasa ta daya wajen tura dakaru cikin tawagogin MDDr, tsakanin dukkanin kasashe mambobin dindindin a kwamitin tsaron MDD.

Daga nan sai Wang ya bayyana aniyar kasar Sin, ta ci gaba da aiki tare da dukkanin kasashe masu son zaman lafiya, wajen ingiza ayyukan wanzar da zaman lafiya da ci gaban duniya. (Saminu)