logo

HAUSA

Shugaban Africa CDC ya gargadi Afirka da ta kiyaye tsauraran matakan rigakafin COVID-19 duk da raguwar sabbin masu kamuwa da cutar

2022-04-18 11:22:32 CMG Hausa

 

Daraktan cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afirka (Africa CDC) John Nkengasong, ya gargadi kasashen Afirka, da su kiyaye tsauraran matakan rigakafin COVID-19, duk da raguwar sabbin masu kamuwa da cuta a halin yanzu.

Nkengasong ya bayyana a yayin da yake ganawa da manema labarai lokaci-lokaci game da yanayin yaduwar cutar a nahiyar cewa, bai kamata raguwar masu kamuwa da cutar a nahiyar Afirka da ma duniya ta yaudare mu ba, hakan ba yana nufin ba za mu sake ganin barkewar cutar ba. Yana mai cewa, mun sha ganin irin wannan yanayi.

Alkaluman da hukumar Afirka CDC ta fitar sun nuna cewa, a tsakanin ranar 11 ga watan Maris zuwa 10 ga watan Afrilu, nahiyar Afirka ta samu raguwar kaso 16 cikin 100 na sabbin masu kamuwa da cutar, idan aka kwatanta da na wata daya da ta gabata. A halin da ake ciki, adadin wadanda suka mutu sanadiyar COVID-19 a wannan lokacin kuma, ya nuna matsakaicin raguwar kashi 2 cikin dari.

A cewar Nkengasong, alkaluman da cibiyar Africa CDC ta yi nazari sun nuna cewa, karancin yanayin yaduwar cutar, galibi ya kan kai tsakanin watanni biyu zuwa uku. (Ibrahim)