logo

HAUSA

Kamfanonin kasar Sin da ke Masar sun baiwa mabukata gudummawa a watan Ramadan

2022-04-18 11:17:47 CMG Hausa

Rahotanni daga kasar Masar na cewa, sama da kamfanonin kasar Sin 30 da ke kasar ne, suka yi amfani da damar watan Ramadan, wajen shirya taron jin kai a birnin Alkahira ranar Asabar din da ta gabata, domin ba da gudummawar Fam miliyan 1 na kasar Masar, kwatankwacin dalar Amurka dubu 54,245, don taimakawa iyalai dake wurin wadanda ke cikin mabukata.

A cewar masu shirya taron, bikin na bana shi na takwas, tun bayan da majalisar 'yan kasuwa ta kasar Sin ta kaddamar a kasar Masar a shekarar 2015. A cikin wadannan shekaru, gudummawar akwatunan kyaututtuka na Ramadan fiye da 10,000 da majalisar ke bayarwa, sun taimakawa sama da iyalai 40,000 da ke fama da talauci.

A jawabinsa yayin bikin, jakadan kasar Sin dake kasar Masar Liao Liqiang ya bayyana cewa, al'ummar kasar Sin suna martaba dabi'ar gargajiya ta karramawa da mayar da alheri, kana kamfanonin kasar Sin, suna koyi da wannan al’ada wajen ba da taimako dake nuna kyakkyawar abota da aminci a tsakanin al'ummomin kasashen biyu.

A nata jawabin shugabar kungiyar raya hadin kai ta kasar Masar Hanaa Ismail, ta gode wa bangaren kasar Sin da shirya wannan biki, tana bayyana cewa, za a raba tallafin ga mabukata a kan lokaci. (Ibrahim)