logo

HAUSA

GDP na kasar Sin ya karu da kashi 4.8 a rubu’i na farko

2022-04-18 11:27:36 CMG Hausa

 

Hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta bayyana cewa, tattalin arzikin kasar ya kama hanyar bunkasa a rubu’i na farkon shekarar 2022 da muke ciki, duk da kalubalen da ake fuskanta daga yanayi mai sarkakiya da ke karuwa a duniya gami da sake bullar cutar COVID-19 a cikin gida.

Alkaluman hukumar kididdigar na nuna cewa, GDPn kasar ya karu da kashi 4.8 cikin dari a kowace shekara a cikin watannin ukun farko, inda ya karu da kashi 4 cikin dari a rubu'i na hudu na bara.

Kakakin hukumar NBS Fu Linghui, ya bayyana a yayin taron manema labarai Litinin din nan cewa, tattalin arzikin kasar, yana gudana yadda ya kamata tare da ci gaba da farfadowa, yayin da kasar ta yi nasarar daidaita matakan yaki da COVID-19, da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.(Ibrahim)