logo

HAUSA

Wakilin Sin ya bukaci a kawo karshen sabon yakin cacar baka

2022-04-18 11:25:33 CMG Hausa

 

Jakadan kasar Sin a kasar Amurka Qin Gang, ya bukaci a dauki matakan da za su warware takaddamar dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka wande ke neman rikidewa zuwa wani sabon yakin cacar baka.

Qin ya yi wannan tsokaci ne a yayin gabatar da jawabi a taron dandalin tattaunawa kan kasar Sin na kwalejin Harvad na HCCF ta kafar bidiyo.

Ya bayyana cewa, jami’ar Harvard tana da dalibai Sinawa sama da 1,000, adadi mafi yawa na dalibai ‘yan kasashen waje, ya bayyana lamarin a masayin wata alama dake bayyana ruhin alaka a tsakanin mutum da mutum tsakanin kasashen Sin da Amurka.

Sai dai kuma, Qin ya bayyana cewa, huldar dake tsakanin kasashen biyu tana kara fuskantar yanayi mai sarkakiya, da kara tabarbarewar dangantaka, da kuma rashin fahimtar juna dake kara kamari a tsakanin kasashen biyu, wanda ke neman zama tamkar wani sabon yakin cacar baka.

Qin ya ce, yana fatan dandalin zai yi amfani da hikimomi, da kuma gabatar da muhimman shawarwari daga bangarorin biyu domin tattauna su, tare da lalubo bakin zaren warware sabani da rashin fahimta dake wanzuwa a tsakanin manyan kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya.

Dandalin tattaunawa kan kasar Sin na kwalejin Harvard wanda aka kafa a shekarar 1997, ya kasance dandalin dalibai mafi girma kuma mafi dadewa dake ba da damar tattaunawa don karawa juna sani game da huldar dake tsakanin Sin da Amurka. Ana gudanar da taron dandalin ne a duk watan Afrilu a jami’ar Harvard.(Ahmad)