logo

HAUSA

Ana jigilar manyan karafun gadar Cocody daga Sin zuwa Kwadibuwa

2022-04-17 16:33:06 CMG Hausa

Jiya Asabar 16 ga wata, jirgin ruwa dakon kaya na farko ya kwashi manya karafuna guda 37 wadanda za a yi amfani da su domin aikin gina gadar Cocody ta kasar Kwadibuwa, gadar mai madaurai mafi girma a yankin yammacin Afirka, ya tashi daga tashar ruwan kogin Yangtse dake birnin Nantong na lardin Jiangsu na kasar Sin, zuwa kasar ta Kwadibuwa.

Gadar Cocody mai tsawon mita 630, muhimmin aiki ne na hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, idan aikin ya kammala, wanda kamfanin kasar Sin ke gudanarwa, za ta kasance gada mai madaurai mafi girma a yankin yammacin Afirka. (Jamila)