logo

HAUSA

Rasha ta kori jami’an diflomasiyyar EU 18

2022-04-16 16:09:36 CMG Hausa

 

Kasar Rasha ta kori jami’an diflomasiyya 18 na Kungiyar Tarayyar Turai EU, a wani mataki na ramuwa.

Wata sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar jiya Jumma’a 15 ga wata, ta ce ma’aikatar da kira shugaban tawagar kungiyar Tarayyar Turai a Rasha wato Markus Ederer domin bayyana korafinta kan matakin da EU ta dauka a farkon wannan wata, na ayyana jami’an diflomasiyyar Rasha 19 a matsayin wadanda ba a amince da su ba, aka kuma tubewa rigar kariya.

Sanarwar ta kara da cewa, a martanin matakin kiyayya da EU ta dauka, ita ma Rasha ta ayyana ma’aikata 18 na tawagar EU a kasarta a matsayin wadanda ba ta amince da su ba, kuma za su bar kasarta nan ba da jimawa ba. (Fa’iza Mustapha)