logo

HAUSA

An bude baje kolin Canton Fair ta yanar gizo cikin yanayi na yaki da annobar COVID-19

2022-04-16 15:57:08 CMG Hausa

An bude baje kolin hajojin da ake shigowa da wadanda ake fitarwa daga kasar Sin ko “Canton Fair” a jiya Juma’a ta yanar gizo, cikin yanayi na yaki da annobar COVID-19.

Baje koli na kwanaki 10, a bana ya samu hallarar sama da masu baje hajoji na cikin kasar Sin da na waje har 25,500. Masu baje kolin za su samu hidimomin yanar gizo daban daban, kamar nuna hajoji ta yanar gizo, da musayar damar kasuwanci, da kuma kaddamar da hajoji.

A cewar kakakin mashirya taron Xu Bing, kamfanoni mahalarta sun gabatar da sama da hajojin tallatawa sama da miliyan 2.9, ciki har da sama da sabbin hajoji 900,000, da kuma sama da hajoji marasa gurbata muhalli 480,000, nau’o’in hajojin da a fanninsu, su ne mafiya yawa da aka taba bajewa a yayin baje kolin da suka gabata.  

Mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin Wang Shouwen ya yi bayyana yayin bikin bude baje kolin cewa, kasar Sin za ta kara bude kofarta ga kasashen waje. Ya ce, yawan kudin cinikin kayayyaki da aka samu a kasar Sin a shekarar 2021 ya zarce dalar Amurka triliyan 6, saurin bunkasar tattalin arzikin kasar kuma ya kai kashi 8.1 cikin dari, wanda ya sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki da cinikayya na duniya. Kana baje kolin Canton Fair zai taka muhimmiyar rawa kan wannan batu.