logo

HAUSA

Kumbon Shenzhou-13 zai baro tashar sararin samaniya

2022-04-15 13:53:42 CMG Hausa

’Yan sama jannatin dake cikin kumbon Shenzhou-13, wanda ya kammala dukkan ayyukansa kamar yadda aka tsara, za su baro tashar sararin samaniya ta kasar Sin ta Tianhe, inda za su sauka a cibiyar saukar kumbuna ta Dongfeng dake yankin Mongolia ta gida dake arewacin kasar Sin.

Tuni ’yan sama jannatin na cikin Shenzhou-13 da suka hada da Zhai Zhigang da Wang Yaping da Ye Gungfu suka shiryawa barin tashar ta sararin samaniya, inda kuma cibiyar Donfeng ke shirye-shiryen tarbarsu.  (Fa’iza Mustapha)