logo

HAUSA

Xi Da Takwaransa Na Mauritius Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kulla Huldar Diflomasiyya

2022-04-15 19:55:33 CMG Hausa

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Mauritius Prithvirajsing Roopun suka yi musayar sakon taya juna murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Xi ya yi nuni da cewa, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu shekaru hamsin da suka gabata, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ta samu ci gaba mai inganci da bunkasa yadda ya kamata, dadaddiyar dangantakar ta haye dukkan wahalhalu, kuma tana kara yin karfi, kana ana kara zurfafa hadin gwiwa a dukkan fannoni.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, yana dora muhimmanci matuka kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Mauritius, kana yana son yin aiki tare da shugaba Roopun, wajen yin amfani da bikin cika shekaru 50 a matsayin wata dama, ta kyautata dadadden zumuncin, da fadada hadin gwiwar moriyar juna, da sa kaimi ga samun ci gaba tare, ta yadda hakan zai amfani kasashen biyu da jama’arsu.

A nasa sakon, shugaba Roopun ya bayyana cewa, fara aiki da kuma aiwatar da yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci tsakanin kasashen biyu, ya kara karfafa dankon zumuncin dake tsakanin kasashen biyu. Roopun ya ce, yana fatan bangarorin biyu za su yi amfani da bikin cika shekaru 50 a matsayin wata dama, ta gano sabbin abubuwa, da karfafa da fadada hadin gwiwa, da zurfafa zumunci da nuna yarda da juna.(Ibrahim)