logo

HAUSA

Najeriya: ’Yan bindiga sun hallaka a kalla mutane 106 a jihar Plateau

2022-04-15 13:49:40 CMG Hausa

Mahukunta a jihar Plateau dake shiyyar tsakiyar Najeriya, sun ce harin da wasu ’yan bindiga suka kaddamar kan wasu kauyukan karamar hukumar Kanam dake jihar a ranar Lahadin karshen makon jiya, ya haddasa rasuwar mutane a kalla 106. A ranar Litinin ne dai aka gudanar da jana’izar mutanen da ’yan bindigar suka hallaka.

Da yake karin haske kan hakan yayin tattaunawa da wata kafar talabijin ta kasar, shugaban karamar hukumar Dayabu Garga, ya ce baya ga wadanda aka hallaka, akwai kuma karin sama da mutum 16 da ke samun kulawar jami’an lafiya a asibiti.

Garga ya ce "A ranar Litinin na halarci jana’izar mutane 106, kuma har yanzu muna gano karin gawawwakin dake warwatse cikin gonaki. Ko shakka babu wannan lamari ne mai matukar tayar da hankali".

Wannan ne dai karon farko da aka bayyana alkaluman wadanda suka rasu a hukumance, yayin tashin hankalin na Kanam, tuni kuma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin na ’yan bindiga.  (Saminu)