logo

HAUSA

Yawan jarin waje a kasar Sin ya karo da kaso 25.6 a rubu’in farko na bana

2022-04-15 13:54:24 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin, ta ce jarin waje da aka yi amfani da shi a babban yankin kasar, ya karu da kaso 25.6, zuwa yuan biliyan 379.87 a rubu’in farko na bana.

A cewar ma’aikatar, idan aka sauya adadin zuwa dalar Amurka, jarin ya karu da kaso 31.7 inda ya kai dala biliyan 59.09.

Karuwar jarin ya zo ne daidai lokacin da ake fuskantar karuwar rashin tabbas a cikin gida da waje, saboda abubuwa da dama, ciki har da sake bullar cutar COVID-19.

Da take tabbatar da tasirin COVID-19 kan harkokin kasuwancin kamfanonin ketare, kakakin ma’aikatar Shu Jueting, ta ce an kafa wani rukuni na musamman da zai kula da muhimman ayyukan da jarin waje ke aiwatarwa, kana ma’aikatar da hukumomin masu ruwa da tsaki a cikin gida, na daukar matakan da suka dace na ganin kamfanonin sun shawo kan kalubalen da suke fuskanta. (Fa’iza Mustapha)