logo

HAUSA

Yadda aka raya garin Yingcheng ta hanyar raya aikin sarrafa wani nau’in abinci na musamman

2022-04-15 16:06:39 CMG Hausa

An shafe shekaru 300 ana sarrafa wani nau’in abincin da ake yi da wake, da shinkafa mai siffar taliya wato Dou Pi, a birnin Yingcheng dake lardin Hubei na kasar Sin.

A shekarar 2014, Cheng Mengxing ta koma garinsu dake birnin Yingcheng na lardin Hubei bayan ta gama karatunta a jami’a, domin raya aikin sarrafa wani nau’in abincin da ake yi da wake, da shinkafa mai siffar taliya wato Dou Pi. Lamarin da ya samar da ayyukan yi ga tsofaffi da mata dake garin, wadanda a baya suka sha fama da talauci.

Haka kuma, ta fara sayar da Dou Pi ta yanar gizo, inda ta dauki wasu daliban jami’a da su sayar da irin wannan kayan abinci. Sakamakon haka, abincin ya samu karbuwa a kasuwa, har ta kara wa dalibai kaimi wajen raya aikin, da kuma ba da gudummawa ga bunkasuwar garuruwansu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)