logo

HAUSA

Xi ya tattauna da yariman Saudiyya da safiyar yau

2022-04-15 14:11:24 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna da safiyar yau Juma’a, da yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman Al Saud ta wayar tarho.

A cewar Xi Jinping, yanzu haka yanayin yankinsu da na duniya na fuskantar manyan kalubale masu sarkakiya. Yana mai bayyana muhimmancin dangantakar dake tsakanin Sin da Saudiyya.

Ya ce kasar Sin na bada muhimmanci ga raya dangantakarta da Saudiyya, kuma a shirye take ta hada hannu da Saudiyyar wajen zurfafa huldarsu da kuma amfanawa kasashen 2 da al’ummominsu. (Fa’iza Mustapha)