logo

HAUSA

MDD ta fitar da dala miliyan 100 domin tallafawa kasashe 7 da tasirin rikicin Ukraine ya fi shafa

2022-04-15 11:25:30 CMG Hausa

MDD ta fitar da dala miliyan 100, daga asusun tallafin gaggawa na CERF, domin taimakawa kasashen Afirka 6 da kasar Yemen, bisa wahalhalun da suke fama da su sakamakon tasirin rikicin Ukraine.

Ana sa ran amfani da kudaden, wajen tallafawa hukumomin MDD da abokan aikinsu, da kudaden samar da muhimman kayan abinci, da kudaden tallafi, da sauran kayan masarufi ga al’ummun Somalia, da Habasha, da Kenya, da Sudan, da Sudan ta Kudu, da Najeriya, sai kuma Yemen, kamar dai yadda ofishin tsare-tsaren ayyukan jin kai na MDDr OCHA ya bayyana.

Da wannan tallafi, asusun CERF ya samar da jimillar kudi sama da dala miliyan 170 ke nan, domin gudanar da ayyukan dakile hauhawar farashin abinci, a kasashen 7 cikin watanni 6 da suka gabata. (Saminu)