logo

HAUSA

An bude baje kolin Canton Fair ta yanar gizo cikin yanayi na yaki da annobar COVID-19

2022-04-15 15:47:22 CMG Hausa

An bude baje kolin hajojin da ake shigowa da wadanda ake fitarwa daga kasar Sin ko “Canton Fair” a yau Juma’a ta yanar gizo, cikin yanayi na yaki da annobar COVID-19.

Baje koli na kwanaki 10, a bana ya hallara sama da masu baje hajoji na cikin kasar Sin da na waje har 25,500. Masu baje kolin za su samu hidimomin yanar gizo daban daban, kamar nuna hajoji ta yanar gizo, da musayar damar kasuwanci, da kuma kaddamar da hajoji.

A cewar kakakin mashirya taron Xu Bing, kamfanoni mahalarta sun gabatar da sama da hajojin tallatawa sama da miliyan 2.9, ciki har da sama da sabbin hajoji 900,000, da kuma sama da hajoji marasa gurbata muhalli 480,000, nau’o’in hajojin da a fanninsu, su ne mafiya yawa da aka taba bajewa a yayin baje kolin da suka gabata.   (Saminu)