logo

HAUSA

Sin: Amurka ba ta da ikon ci gaba da gudanar da ayyukanta na soja da suka shafi binciken kwayoyin halitta

2022-04-14 19:44:43 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya shaidawa taron manema labaru da aka saba yi Alhamis din nan cewa, ya zuwa yanzu Amurka ba ta bayar da gamsasshen bayani kan ayyukanta na soja kan kwayoyin halitta da take yi ba.

Magance matsaloli ta hanyar tuntubar juna da hadin kai, na daga cikin ka’idojin yarjejeniyar takaida yaduwar makamai masu guba (BWC) kuma Amurka ba ta da ikon kaucewa wannan batu.

Zhao Lijian ya jaddada cewa, a matsayinta na daya daga cikin kasashen da ke cikin yarjejeniyar, kamata ya yi Amurka ta kasance abin koyi wajen martaba ka'ida, ba wai kaucewa doka ba. Kasar Sin tana sake yin kira ga kasar Amurka, da ta yi bayani dalla-dalla game da ayyukanta na soji da suka shafi kwayoyin halitta, da kuma daina nuna adawa da kafa wani tsarin hadin gwiwar sanya ido tsakanin bangarori daban-daban.(Ibrahim)