logo

HAUSA

Bankin duniya ya yi hasashen raguwar bunkasar tattalin arzikin yankin kudu da hamadar Sahara zuwa kaso 3.6 bisa dari

2022-04-14 10:46:21 CMG Hausa

A jiya Laraba, bankin duniya ya yi hasashen raguwar bunkasar tattalin arzikin yankin kudu da hamadar Saharar Afirka zuwa kaso 3.6 bisa dari a shekarar nan ta 2022, sabanin kaso 4 bisa dari da yankin ya samu a shekarar bara.

Bankin duniya ya ce, tattalin arzikin yankin na hankoron farfadowa, duk da tafiyar hawainiya da bangarorin tattalin arzikin sa ke fuskanta, da kalubale a fannin samar da hajoji, da barkewar sabbin nau’ikan annobar COVID-19, da hauhawar farashin kayayyaki, da karuwar hadurra a fannin hada hadar kudade sakamakon matsalolin samar da lamuni.

Bankin duniyar ya shaida hakan ne, cikin rahoton sa na sakamakon wani binciken da ya fitar, mai taken "Ci gaban tattalin arziki a yankin zai ragu a bana, yayin da ake fuskantar nau’o’in wahalhalu a sassan duniya, da rashin tabbas da ake fama da shi”.  (Saminu)