logo

HAUSA

Li Keqiang: Sin za ta rungumi salon ci gaba bisa daidaito a fannin cinikayyar waje

2022-04-14 13:42:32 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ce, gwamnatin Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufofin bunkasa cinikayyar waje, a matsayin daya daga ginshikan daidaitawa, da inganta rayuwar al’ummar kasar.

Hakan dai sakamako ne na taron majalissar gudanarwar kasar Sin, wanda firaminista Li Keqiang ya jagoranta a jiya Laraba. Kaza lika taron ya amince da bukatar aiwatar da manufar tallafawa hada-hadar fitar da hajoji zuwa ketare, domin bunkasa cinikayyar waje ta Sin.

Har ila yau, an amince da aiwatar da matakan dakile tasirin annobar COVID-19, da bunkasa farfadowa da ci gaban sayayyar hajojin waje.

Taron ya ce, domin saukaka wahalhalun da kamfanonin ketare ke fuskanta yayin cinikayya, da burin bunkasa daidaito a fannonin shige da ficen hajoji, za a kara inganta matakan samar da rangwame a fannin haraji, mai dacewa da dokokin kasa da kasa, tare da kara inganta yanayin muhallin gudanar da hada-hadar kasuwanci da sassan ketare daga bangarori daban daban. (Saminu)