logo

HAUSA

Xi Ya Ba Da Umarnin Gina Wurin Harba Kumbon Wenchang Da Babu Kamarsa A Duniya

2022-04-14 20:23:28 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci da a kara kaimi wajen ganin an daga matsayin wurin harba kumbunan sama jannati da ke tsibirin Hainan na kudancin kasar Sin, da babu kamarsa a duniya.

Xi ya bayyana haka ne, lokacin da ya ziyarci wurin harba kumbon sararin samaniya na Wenchang ranar Talata.

Bayan da aka yi masa bayani, Shugaba Xi ya duba hasumiyar da ake harba kumbunan da sauran wurare. Ya kuma yi bayani sosai game da jerin muhimman ayyukan harba kumbuna zuwa sararin samaniya da aka kaddamar daga wurin, wadanda suka hada da harba muhimmin bangare na tashar sararin samaniya ta Tianhe, da aikin harba na’urar binciken duniyar wata ta Chang'e-5, da kumbon binciken duniyar Mars ta Tianwen-1.

Xi ya kuma lura cewa, Wenchang shi ne wurin harba roka na zamani na kasar Sin, kuma shi ne gadar binciken sararin samaniyar kasar mai zurfi.

Don haka, a cewar shugaba Xi, ya kamata wurin harba kumbunan sararin samaniyar, ya ci gaba da sanya ido kan tsarin ci gaban binciken sararin samaniyar duniya, da muhimman bukatun masana'antar binciken sararin samaniyar kasar Sin, da inganta karfinta na harba kumbunan binciken sararin samaniya na zamani baki daya. (Ibrahim)