logo

HAUSA

Ba zai yiwu a zargi yanayin kare hakkin dan Adam na Sin bisa wani rahoton Amurka ba

2022-04-13 20:39:05 CMG Hausa

Majalisar harkokin wajen kasar Amurka ta fitar da rahoton kare hakkin dan Adam dake shafar kasa da kasa na shekarar 2021 a jiya, inda a ciki ta zargi tsarin siyasa da yanayin kare hakkin dan Adam na kasar Sin. Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya yi nuni a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, abubuwan da ta wallafa dake shafar kasar Sin a cikin rahoton da ra’ayin sakataren harkokin wajen kasar Amurka game da Sin ba su da tushe, cike suke da karya da ra’ayin nuna bambanci ga Sin, don haka Sin tana adawa da su.

Zhao Lijian ya bayyana cewa, Sinawa da kansu suna da iznin yin magana kan yanayin kare hakkin dan Adam na kasar, kana kasa da kasa sun ga yadda gwamnatin kasar Sin take gudanar da ayyukanta a kasar. Wannan ba wani abu ba ne da wani zai zargi Sin a wannan fanni ta hanyar yin magana ko bayar da wani rahoto. Gwamnatin kasar Amurka ta kan fitar da irin wannan rahoto a kowa ce shekara don zargi yanayin kare hakkin dan Adam na Sin, a kokarin mayar da kanta a matsayin mai yanke hukunci kan batun kare hakkin dan Adam, hakan ya fallasa manufuncin kasar Amurka ta nuna ma’auni biyu kan wannan batu. (Zainab)