logo

HAUSA

Darajar kayayyakin da Sin ta shigo da fitar da su zuwa kasashen dake aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” ta kai Yuan tiriliyan 2.93 daga Janairu zuwa Maris

2022-04-13 14:21:10 CMG Hausa

Yau Laraba da safe, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira taron manema labarai, inda kakakin babbar hukumar kwastam ta kasar, wanda kuma shi ne shugaban sashin nazarin alkaluman kididdiga, Li Kuiwen ya gabatar da bayani game da harkokin shige da fice na watan Janairu zuwa Maris din bana.

Alkaluman hukumar sun nuna cewa, a watan Janairu zuwa Maris din bana, darajar kayayyakin da kasar Sin ta shigo da fitar da su zuwa kasashen dake aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” ta kai kudin Sin Yuan tiriliyan 2.93, wanda ya karu da kaso 16.7 bisa dari, ciki har da Yuan tiriliyan 1.64 na kayayyakin da ta fitar zuwa ketare, wanda ya karu da kaso 16.2 bisa dari, sa’annan da Yuan tiriliyan 1.29 na kayayyakin da ta shigo da su, wanda ya karu da kaso 17.4 bisa dari. (Murtala Zhang)