logo

HAUSA

Sin: Amurka babbar barazana ce ga tsaron sararin samaniya

2022-04-13 20:43:42 CMG Hausa

 

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyanawa taron manema labaru na yau da kullum Larabar nan cewa, Amurka ce babbar barazana ga tsaron sararin samaniya. Don haka, ya dace gwamanatin Amurka ta himmantu wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta a matsayinta na babbar kasa, kana ta sake duba jerin ayyukanta marasa dacewa a fagen sararin samaniya.

Kalaman na Zhao na zuwa ne, bayan da ma’aikatar tsaron Amurka ta fitar da rahoto kan abin da ta kira “barazana a sararin samaniya daga Sin da Rasha”

Zhao Lijian ya ce, gwamnatin Amurka ta fito karara ta ayyana sararin samaniya a matsayin wani 'yankin yaki', har ma ta hanzarta kafa rundunar sojan sama da ta sararin samaniya, da kuma kerawa da ma tura makamai a sararin samaniya. A matsayinta na kasar da ke da dubban taurarin dan Adam, har yanzu kasar Amurka na ci gaba da harba taurarin dan Adam daban-daban zuwa sararin samaniya, ciki har da tauraron dan Adam na leken asiri na aikin soja.

Haka kuma, sojojin Amurka suna da hannu dumu-dumu a cikin manyan jarin harkokin kasuwanci a sararin samaniya, suna sayan taurarin dan Adam na kasuwanci na biliyoyin daloli don amfanin ayyukan soja. A sa'i daya kuma, kasar Amurka ta dade tana nuna adawa da shawarwarin da aka yi game da takaita yaduwar makamai a sararin samaniya, abin da ya sanya ta zama babbar matsala ga tsarin sarrafa harkokin binciken sararin samaniya.(Ibrahim)