logo

HAUSA

A kalla mutane 16 ne suka jikkata yayin harin bindiga a tashar jirgin karkashin kasa ta Brooklin na Amurka

2022-04-13 10:11:41 CMG Hausa

Rundunar ’yan sandan birnin New York na Amurka, ta tabbatar da rasuwar mutane 16, da jikkatar wasu da dama, ciki har da mutane 10 da harsashin bindiga ya samu, sakamakon harin bindiga a tashar jirgin kasan karkashin kasa dake unguwar Brooklin ta birnin da safiyar jiya Talata.

A cewar rundunar, da misalin karfe 8:24 na safiya, lokacin da wani jirgin kasa ke tsayawa a tashar dake kusa da Sunset Park, wani mutum da ya rufe fuskarsa, sanye da rigar ma’aikatan gine-gine, ya bude wuta kan mutanen dake cikin jirgin, da ma wadanda suke waje kusa da jirgin. ’Yan sanda sun ce za su kara tsananta bincike game da musabbabin aukuwar harin.

Da take karin haske kan hakan, mataimakiyar kwamishinan ’yan sandan birnin Laura Kavanagh, ta shaidawa manema labarai cewa, 5 daga cikin wadanda aka harba na cikin halin mutu kokwai rai kokwai.

A daya hannun kuma, an yiwa shugaban Amurka Joe Biden, cikakken bayani game da aukuwar wannan lamari, kamar dai yadda wata majiyar fadar White House ta tabbatar.   (Saminu)