logo

HAUSA

Wajibi ne Pelosi ta soke ziyarar da ta shirya kaiwa Taiwan

2022-04-13 14:24:29 CMG Hausa

A yau Laraba 13 ga wata, ofishin dake lura da harkokin yankin Taiwan na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya kira taron ’yan jaridu. Inda kakakin ofishin Ma Xiaoguang ya yi kira ga al’ummar Sinawa na bangarorin zirin Taiwan, da su aiwatar da matakan dakile kudurin ballewar yankin Taiwan. A hannu guda kuma, ya ja hankalin kakakin majalissar wakilan Amurka Nancy Pelosi, da ta soke shirin ta na ziyartar yankin na Taiwan.

Ma ya kara da cewa, ya kamata Amurka ta aiwatar da bangaren ta na sanarwa 3 da ta amince tare da Sin, game da manufar kasar Sin daya tak a duniya, ta kuma cika alkawarin da ta daukarwa Sin, don gane da batun Taiwan. Ya ce “Za mu tsaya haikan wajen yakar duk wani mataki da zai lahanta ikon mulkin kai da tsaron yankunan kasarmu”.

Ma Xiaoguang, ya kuma baiwa jam’iyyar DPP mai mulki a Taiwan shawarar sauya matsaya, ta hanyar rungumar matsayar da aka cimma a shekarar 1992, tare da aiwatar da matakai na hakika, na dora alakar sassan na zirin Taiwan kan turba ta gari.   (Saminu)