logo

HAUSA

Mutane 23 sun rasu yayin harin da aka kai wasu kauyuka biyu dake tsakiyar Najeriya

2022-04-13 09:50:38 CMG Hausa

A jiya Talata, kakakin gwamnan jihar Benue dake shiyyar tsakiyar Najeriya ya bayyana cewa, a daren Litinin din da ta gabata, wasu ‘yan bindiga sun kai wa kauyukan Guma, da Tarka dake jihar hari, inda suka hallaka a kalla mutane 23, kana wasu da dama sun jikkata, kuma yanzu haka an riga kai wadanda suka jikkata asibitin domin samun jinya.

Kakakin ya kara da cewa, gwamnan jihar ya soki harin da kakkausar murya, kuma ya bukaci hukumomin tsaro da su dakile makaman da ake amfani da su ba bisa ka’ida ba, kana ya yi kira ga al’ummun jihar da su goyi bayan ayyukan da rundunar tsaro za ta gudanar. (Jamila)