logo

HAUSA

Putin: Rasha da Belarus za su kara karfafa cudanya domin dakile takunkumin kasashen yamma

2022-04-13 10:37:58 CMG Hausa

Jiya Talata shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, da takwaransa na kasar Belarus Alexander Lukashenko, sun shirya taron manema labarai na hadin gwiwa, a filin harba taurarin dan adama dake gabashin Rasha, inda shugaba Putin ya bayyana cewa, kasarsa da Belarus za su kara karfafa cudanyar tattalin arzikin dake tsakaninsu, ta yadda za su dakile takunkumin da kasashen yamma suke kakaba musu, kana ya ce kasar Belarus, dandali ne mai dacewa ga Rasha na yin shawarwari da Ukraine.

A nasa bangaren, shugaba Lukashenko ya bayyana cewa, kasar Amurka tana shawo kan Ukraine, da Poland, da kasashe uku dake gabar tekun Baltic, wato Estonia, da Latvia, da Lithuania, domin su yaki Belarus, don haka Belarus din za ta hana duk wata dama ta yakar Rasha, yayin da kasar ke gudanar da aikin soji na musamman. (Jamila)