logo

HAUSA

Xi ya jaddada tabbatar da ingancin iri wajen samun wadatar abinci a kasa

2022-04-13 08:39:57 CMG Hausa

A wannan makon ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci dakin gwaje-gwajen iri na Yazhou Bay, da kwalejin nazarin teku na jami'ar Sanya ta kasar Sin da ke birnin Sanya na lardin Hainan, domin fahimtar yadda Hainan ke samar da goyon baya ga ayyukan kirkire-kirkire a masana'antar iri da ma bunkasa fasahar teku. Wannan shi ne karo na uku da shugaba Xi Jinping ya ziyarci Hainan cikin shekaru goma da suka gabata.

Xi Jinping, ya jaddada muhimmiyar rawar da irin shuka yake takawa a kasar Sin wajen tabbatar da wadatar abinci a kasar. Yana mai cewa, kiyaye albarkatun tsirrai a cikin gida, ita ce hanya daya tilo ta tabbatar da wadatar abinci a kasar. Ya ce, idan har ana son tabbatar da ingancin albarkatun irin shuka, dole ne kasar ta kasance mai tsayawa da kafafunta a fannin fasahar irin shuka. Ya kuma yi kira da a daukaka ruhin tsoffin masana kimiyya da masu bincike, ciki har da Yuan Longping.


Haka kuma shugaba Xi ya ziyarci cibiyar nazarin halittun teku ta birnin Sanya ta jami’ar teku ta kasar Sin dake birnin Sanya na lardin Hainan na kasar Sin, domin kara fahimtar yadda ake goyon bayan kirkire-kirkire a lardin, da raya kimiyya da fasahar teku a lardin.

A shekarar 2018 ne, lardin Hainan ya yi bikin cika shekaru 30 da kafa yankin tattalin arziki na musamman. A yayin da ya halarci bikin, Xi Jinping ya sanar da babbar shawarar da aka yanke ta ba da goyon baya ga kafa yankin ciniki cikin 'yanci na gwaji a Hainan, inda ya zana tsarin ci gaban Hainan a sabon zamani.


Xi Jinping ya bukaci masu kaunar gina Hainan, da su shiga cikin sabon shirin ci gaban lardin. Kaunar da Xi Jinping ke yiwa wannan tsibiri, za ta bar sabbin abubuwan tunawa da ba za a taba mantawa da su ba. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)