logo

HAUSA

Xi Jinping ya ziyarci yankin raya tattalin arziki na Yangpu dake lardin Hainan

2022-04-13 13:37:06 CMG Hausa

Jiya Talata, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar, Xi Jinping ya yi rangadin aiki a yankin raya tattalin arziki na Yangpu dake birnin Danzhou na lardin Hainan.

Yankin raya tattalin arziki na Yangpu, yanki ne na farko da baki ‘yan kasashen waje suka zuba jari don rayawa, inda kuma ake more manufofin gatanci a fannin buga harajin kwastam.

A shekara ta 2021, jimillar GDPn yankin Yangpu ta kai kudin Sin Yuan biliyan 43.66, abun da ya karu da kaso 34.2 bisa dari. An kaddamar da wasu hanyoyin zirga-zirgar jiragen ruwan kasuwanci 39 a yankin, wadanda suka shafi wasu muhimman tashoshin jiragen ruwa dake kasar Sin, da na kasashen kudu maso gabashin nahiyar Asiya.(Murtala Zhang)