logo

HAUSA

Sin tana adawa da yadda Amurka ta siyasantar da batun janye jami’anta

2022-04-12 21:16:15 CMG Hausa

Game da batun yadda kasar Amurka ta janye jami’anta daga karamin ofishin jakadancinta dake birnin Shanghai, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau cewa, Sin tana adawa da yadda Amurka ta siyasantar da batun janye jami’anta, kuma ta gabatar da korafi ga kasar Amurka. Ya kamata kasar Amurka ta daina nuna kiyayya ga manufofin Sin na magance yaduwar cutar COVID-19, da siyasantar da batun, da kuma zargin kasar Sin ba tare da wata hujja ba.

A yau ne, a shafin yanar gizo na ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka dangane da shawara kan yin yawon shakatawa a Sin, ta bayyana cewa, kasar Amurka ta bukaci karamin ofishinta dake birnin Shanghai da ya janye jami’ai da ma’aikata da iyalansu da ba na gaggawa ba, wannan ya shaida cewa, kasar Amurka ta tilastawa jami’an da ma’aikatansu su janye daga birnin Shanghai a maimakon ba su umarni tukuna.

Zhao Lijian ya jaddada cewa, manufofin Sin na magance yaduwar cutar COVID-19 suna da tasiri da inganci a fannin kimiyya. Sin tana da imani game da samun nasarar yaki da cutar a birnin Shanghai, ‘yan kasashen waje dake birnin Shanghai ciki har Amurkawa, suna yin kokari tare da mazauna Shanghai wajen yaki da cutar. (Zainab)