logo

HAUSA

Duba! Wadannan su ne masu samar da guba cikin duniya daga kasar Amurka

2022-04-12 16:22:36 CMG Hausa

Idan muka shiga babban ginin majalisar dokokin kasar Amurka, za a ga shirye-shirye daban daban dake nuna yabo ga tsarin kasar Amurka, inda aka mai da tsarin a matsayin tsari mafi kyau cikin duniya. Amma, cikin tarihin kasar Amurka, ba ta taba daina yake-yake, da tayar da tashe-tashen hankula a tsakanin kabilu ba.

Musamman ma, bayan yakin duniya na biyu, kasar Amurka ta fara haddasa tashe-tashen hankula tsakanin kasa da kasa, yayin da take haddasa sabani a tsakanin kabilu daban daban, har ma da samar da cututtuka masu yaduwa cikin duniya.

Kana, sau da dama, ta taba amfani da makamai masu guba cikin yake-yake, da gina dakunan gwaje-gwajen hallitu cikin kasashen waje, da kuma kawo sabani a tsakanin kabilu daban daban cikin kasa daya. Ana iya cewa, kasar Amurka kasa ce dake samar da guba ga hankulan bil Adama, da ma jikunan bil Adama. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)