logo

HAUSA

Mujallar Fortune: Tattalin arzikin Amurka zai iya samun karaya a 2023

2022-04-12 10:33:40 CMG Hausa

Manyan hamshakan masu zuba jari, da tsoffin manyan shugabannin babban bankin kasa, da kuma manyan bankunan zuba jari sun sha yin gargadin cewa, mai yiwuwa ne Amurka ta fuskanci karayar tattalin arziki a shekarar 2023, kamar yadda mujallar Fortune ta wallafa.

A wani sharhin da mujallar Washington Post ta wallafa a ra’ayin tsohon sakataren baitilmalin Amurka Lawrence Summers, ya nuna cewa, sama da shekaru 75 da suka gabata, a tsawon lokaci tsadar farashi yana karuwa da kashi 4, sannan matsalar rashin aiki ya yi kasa da kashi 5 bisa 100, tattalin arzikin Amurka yana fuskantar koma baya a cikin shekaru biyu, a cewarsa.

Rahoton ya ce, Summers ya jaddada cewa, yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki, ba batu ne da za a iya boyewa ba a bisa yanayi na karayar tattalin arzikin da kasar Amurkar ta fuskanta a lokutan baya a tarihi. (Ahmad)