logo

HAUSA

Yadda Amurka ta kware wajen fadin karya

2022-04-12 16:33:18 CMG Hausa

Idan muka duba yadda kasar Amurka ta haddasa yake-yake a wasu kasashen duniya, za mu gane cewa, ta kan fara ne da fakewa da wasu hujjoji masu karfi, domin ruruta wutar tashe-tashen hankulla a wasu kasashe. Har kullum, a cewarta, tana neman shimfida mulkin “dimokuradiyya” da “adalci” ne a duniya.

Maganganun karya da ’yan siyasan kasar Amurka da kafofin watsa labaran kasar suke fada, suna bata ran al’ummomin kasa da kasa, musamman ma, wadanda suke kaunar zaman lafiya. (Maryam)