logo

HAUSA

Dai Bing ya yi kira da a kawo karshen rikicin Ukraine domin kare rayukan mata da kananan yara

2022-04-12 14:28:18 CMG Hausa

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing ya yi kira da a gaggauta kawo karshen rikicin kasar Ukraine domin shawo kan yanayin jin kai mai muni, da kuma ceto rayukan mata da kananan yaran kasar.

Dai ya ce mata da yara kanana ne a sahun gaba wajen fuskantar mummunan tasirin yaki, don haka ya zama wajibi a lura da batun kare su, yayin da ake dauki ba dadi. A cewar jami’in, "Tattaunawa da gudanar da shawarwari su ne kadai hanyoyin wanzar da zaman lafiya. Muna goyon bayan dukkanin sassa masu ruwa da tsaki, da su ci gaba da tattaunawa, su kara azama wajen shawo kan wahalhalu da sabani, tare da samar da yanayi da zai kai ga dakatar da bude wuta".

Dai Bing ya kara da cewa, kakaba takunkumai, da tura karin makamai ba za su wanzar da zaman lafiya ba. Maimakon hakan, matsa gaimi wajen sanya takunkumai, ya haifar da matsalolin makamashi da abinci, da hauhawar farashin kayayyakin masarufi, wanda dukkanin al’ummun duniya ke fama da shi. Gwamman miliyoyin mata da kananan yara, a kasashe kamar Afghanistan, da Yemen, da sassan kahon Afirka, da yankin Sahel, na kan gaba wajen dandana kuda, sakamakon wannan mataki.  (Saminu)