logo

HAUSA

Jakadan Sin ya yi kira da a rungumi tsarin cudanyar dukkanin sassa wajen yaki da annobar COVID-19

2022-04-12 10:13:10 CMG Hausa

A jiya Litinin, jakadan dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira da a rungumi hakikanin tsarin cudanyar dukkanin sassa, wajen yaki da annobar COVID-19, da kuma shirin farfadowa bayan wucewar ta.

Jami’in ya ce cikin shekaru 2 da ake fama da wannan annoba, sama da mutane miliyan 6 sun rasu. Wannan darasi ne da ya kamata a maida hankali a kan sa.

Zhang Jun, ya shaidawa zaman kwamitin tsaron MDD game da yaki da cutar COVID-19 da rigakafinta cewa, "Ba wani abu mafi muhimmanci da ya zarce rayuwar bil adama. Don haka mayar da al’umma gaban komai muhimmin mataki ne da zai saita alkiblar mu".

Jami’in ya kara da cewa, sama da kowane lokaci, a yanzu duniya na matukar bukatar cudanyar dukkanin sassa. Kaza lika bayan wucewar annobar, ya zama wajibi dukkanin kasashe su karfafa hadin gwiwa karkashin tutar MDD, su martaba juna, da amincewa da juna, da gaskata juna. Su kuma nuna kyakkyawan fata, da hadin gwiwa don cimma moriya tare, su kuma yi aiki tare domin gaba.  (Saminu)