logo

HAUSA

Kasar Sin ta taya Shahbaz Sharif murnar zama sabon firaministan Pakistan

2022-04-12 20:13:28 CMG Hausa

 

            

Talatar nan kasar Sin ta taya Shahbaz Sharif murnar zama firaministan kasar Pakistan, inda ta bayyana fatan kara samun kusancin alaka tsakanin Sin da Pakistan.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana cewa, Sin da Pakistan abokan hadin gwiwa ne bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, kuma dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, tana da karfi, kuma babu wanda zai lalata ta .

Zhao ya ce, kasar Sin na fatan yin aiki tare da bangaren Pakistan, don ci gaba da sada dadadden zumuncin dake tsakaninsu, da zurfafa hadin gwiwa a dukkan fannoni, da gina hanyar tattalin arziki mai inganci tsakanin kasashen Sin da Pakistan yadda ya kamata, da gina al'ummar Sin da Pakistan mai kyakkyawar makoma a sabon zamani.(Ibrahim)