logo

HAUSA

Kasar Sin Na Cikin Lokaci Mai Sarkakkiya A Yaki Da COVID-19

2022-04-12 20:03:58 CMG Hausa

Mai magana da yawun hukumar lafiya ta kasar Sin Mi Feng, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da ka’idojin gama gari na yaki da annobar COVID-19, yayin da kasar ke cikin lokaci mai sarkakkiya a yaki da annobar.

Mi Feng ya shaidawa taron manema labarai da aka shirya Talatar nan cewa, a halin yanzu, cutar na ci gaba da yaduwa da kuma fadada, yana mai cewa, ya zuwa jiya Litinin, an ba da rahoton mutane 1,252 da suka kamu da cutar a babban yankin kasar Sin sai kuma mutane 23,295 da suka kamu da cutar ba tare da nuna alamomi ba a cikin gida.

Mi ya jaddada muhimmancin daukar matakan gaggawa, ciki har da gwajin cutar, da kafa cibiyoyin killace masu kamuwa da cutar, da jinyar wadanda suka kamu da cutar, ta yadda za a dakile hanyoyin yaduwarta nan da nan.

Ya kuma bukaci a kara kaimi wajen samar da kayayyakin bukatun yau da kullum, da biyan bukatun jama’a a fannin magunguna da jinya.

Ya zuwa yanzu, hukumar lafiya ta kasar Sin, ta aike da jami'an kiwon lafiya sama da 40,000 daga larduna 16 na kasar, da kara karfin yi wa mutane miliyan 2.38 gwajin cutar a kowace rana, don tallafawa birnin Shanghai, aiki da ma’aikatan lafiya a birnin wajen gudanar da jinyar masu kamuwa da ma gwajin cutar . (Ibrahim)