logo

HAUSA

Yadda Shugaba Xi Jinping ke kaunar tsiribin Hainan

2022-04-11 19:44:34 CMG Hausa

A yammacin jiya ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci dakin gwaje-gwajen irin hatsi na Yazhouwan, da kwalejin nazarin halittun teku ta birnin Sanya ta jami’ar teku ta kasar Sin dake birnin Sanya na lardin Hainan, domin fahimtar yadda Hainan ke samar da goyon baya ga ayyukan kirkire-kirkire a masana'antar iri da ma bunkasa fasahar teku. Wannan shi ne karo na uku da shugaba Xi Jinping ya ziyarci Hainan cikin shekaru goma da suka gabata. 

A kantar littattafai da ke ofishin Xi Jinping, ana iya ganin hotonsa da mahaifinsa a lokacin da yake matashi. Wannan wani abin tunawa ne mai muhimmanci da Xi Jinping ya bari a lokacin da ya ziyarci mahaifinsa a Hainan a shekarar 1979. A wancan lokacin, Hainan tsibiri ne mai fama da talauci da koma baya. A cikin shekaru 40 da suka gabata, Xi Jinping ya shaida yadda wannan karamin tsibiri, ya kasance tsibirin yawon shakatawa na kasa da kasa da ke da fa'ida ta musamman. 

A watan Afrilun shekarar 2013, Xi Jinping ya shiga jirgin kamun kifi a garin Tanmen, inda ya tambayi masunta game da yadda suke kamun kifi da samun kudaden shiga, inda ya yi masu sahihin fatan alheri.

“A wannan karo ku sake dawowa lafiya, ina taya ku murna, tare da fatan alheri a duk lokacin da kuka je teku."

 A lokacin da ya ziyarci rukunin masana'antu na Yalongwan kuwa, Xi Jinping ya zanta da mazauna kauyukan da ke aiki a wurin. Yana mai cewa, ci gaban al’umma mai wadata, ya dogara ga mazauna kauyen.

 A watan Afrilun shekarar 2018 ne, Xi Jinping ya ziyarci kauyen Shicha dake birnin Haikou, inda ya yaba da ci gaban kauyen na Shicha. 

“ya kamata hanyar farfado da kauyuka ta dogara kan masana’antu, kana raya masana’atun ta kasance tana da sigoginta na musamman. Haka kuma ya dace a yi amfani da hanyar raya kimiyya da ta dace da halin da muke ciki.”

 A shekarar 2018 ne, lardin Hainan ya yi bikin cika shekaru 30 da kafa yankin tattalin arziki na musamman. A yayin da ya halarci bikin, Xi Jinping ya sanar da babbar shawarar da aka yanke ta ba da goyon baya ga kafa yankin ciniki cikin 'yanci na gwaji a Hainan, inda ya zana tsarin ci gaban Hainan a sabon zamani.

 Shugaba Xi Jinping ya bukaci masu kaunar gina Hainan, da su shiga cikin sabon shirin ci gaban Hainan. Kaunar da Xi Jinping ke yiwa wannan tsibiri, za ta bar sabbin abubuwan tunawa da ba za a taba manta da su ba.